Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Aikin Titin N4.47 Biliyan a Sule Tankarkar, Jihar Jigawa

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ƙaddamar da wani aikin babbar hanya mai darajar ₦4.47 biliyan a ƙaramar Hukumar Sule Tankarkar. 
(Barau da Namadi)

Wannan mataki na daga cikin manyan ayyukan inganta ababen more rayuwa da gwamnatin ta sanya gaba don raya jihar.

Ya bayyana cewa aikin zai sa a samu sauƙin Sufuri, haɗin kai tsakanin ƙauyuka da kasuwanni, da kuma ƙara samun ci gaban jama’a.
(Namadi zai bude hanyar?

 Haka zalika, yana daga cikin shirin gwamnati na tabbatar da cewa ƙarshen shekarar nan za a ga sakamako mai amfani ga al’umma.

Kwamishinan aiki ya ce aikin zai haɗa da sabunta hanyar, samar da tsare-tsare don hana ambaliya ko lalacewa, tare da inganta masana’antu da harkokin noma a yankin.
(Namadi)

 A ƙarshe, an umurci jami’an gwamnati da masu aikin su tabbatar da cewa aikin ya ƙare cikin lokaci da inganci.

(Radio Nigeria Kaduna)

Post a Comment

0 Comments