Gwamna Dauda Lawal Ya Jaddada Kudurin Gwamnatinsa Na Kawar da Matsalar Tsaro a Zamfara

(Dauda Lawal)

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa tana da cikakken ƙuduri na kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta dade tana addabar jihar, tare da tabbatar da zaman lafiya ga kowa da kowa.

Yayin taron Majalisar Zartarwa karo na 18 da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Gusau, Gwamna Lawal ya ce ya zama wajibi ga kowane ɗan jihar da ke da ikon taimakawa wajen tsaro ya bada gudunmawa, domin nasarar yaki da rashin tsaro aiki ne na haɗin gwiwar kowa da kowa.

A cewarsa, “Ya kamata mu fahimci cewa wannan gwamnati ta hau bisa alƙawarin dawo da zaman lafiya, kuma dole ne mu tsaya tsayin daka wajen ganin mun cimma wannan buri.”

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa ta dauki matakai masu ƙarfi wajen tallafawa jami’an tsaro, samar da kayan aiki, da ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma a ƙananan hukumomi.

Ya kuma yi kira ga ‘yan majalisar zartarwa da shugabannin al’umma su ci gaba da kasancewa cikin jama’a, su saurari matsalolinsu, domin samun sahihin bayani kan halin da ake ciki a kowane yanki.

A ƙarshe, Gwamna Lawal ya tabbatar da cewa gwamnatin Zamfara ba za ta huta ba sai an tabbatar da cewa duk wani yanki na jihar ya samu cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments