Hukumar Bada Bashin karatu ta kasa (NELFUND) ta Bada damar fara Rijistar Shekarar Karatu 2025/2026.

Hukumar NELFUND Ta Bude Portal Don Neman Lamunin Dalibai Na Shekarar Karatu 2025/2026.
(Nelfund)

Hukumar bada lamunin karatu ta ƙasa, Nigerian Education Loan Fund (NELFUND), ta sanar da bude portal ɗinta na musamman domin dalibai su nemi lamuni na zangon karatu na 2025/2026.

A sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa wannan shirin na nufin tallafawa ɗalibai masu karatu a jami’o’i, kwalejojin ilimi, da sauran makarantun gaba da sakandare, domin rage musu nauyin kuɗin makaranta da kula da karatu.

An ce tsarin lamunin ba shi da riba (interest-free loan), kuma ɗalibai na iya cikawa da kansu ta hanyar shafin: 👉🏽

Haka kuma, hukumar ta bayyana cewa biyan lamunin zai fara ne bayan shekaru biyu da ɗalibai suka kammala aikin NYSC, domin basu damar samun aiki kafin fara biya.

Hukumar ta yi kira ga dukkan jami’o’i da kwalejoji su tabbatar da cewa sun tura jerin sunayen ɗalibai da ke da cancanta kafin a kammala tantancewa.

Abin Lura:

Akwai lokacin ƙayyadadden wa’adin nema, don haka dalibai su gaggauta cikawa kafin ƙofa ta rufe.

Duk wanda ke da matsala wajen cikawa na iya tuntuɓar hukumar kai tsaye ta adireshin shafin su: https://nelf.gov.ng

 “Manufar Wannan Bashin ita ce tabbatar da cewa kowa zai samu damar karatu ba tare da tsoron kuɗi ba,” in ji hukumar NELFUND.

Post a Comment

0 Comments