Babu wata kotu a Najeriya da take da ikon tilastawa mutum yin aure da wani - Kungiyar Lauyoyi. Nijeria

Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta bayyana ɓacin rai da damuwa kan rahoton da ke cewa wata Kotun Majistare a Kano ta bayar da umarni cewa a ɗaurawa fitattun masu amfani da kafar TikTok, Ashiru Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda aure cikin kwanaki 60, sakamakon wata shari’a da ta samo asali daga fitar da bidiyon Rashin da'a da suke yi a tiktok.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya fitar a ranar Talata.

NBA ta bayyana cewa matakin kotun ya nuna rashin fahimtar iyakar ikon shari’a bisa tsarin mulkin ƙasar, tare da zama abin da ke take haƙƙin ɗan Adam da ’yancin mutum na yin zabi.

Kungiyar ta jaddada cewa:

“Babu wata kotu a Najeriya da take da ikon tilastawa mutum yin aure da wani. Wannan lamari ya saɓawa tsarin mulki kuma ba shi da wata hujjar doka.”

A cewar ƙungiyar, aure ya kasance al’amari ne na son rai da yardar juna tsakanin mutane biyu, ba abin da za a iya amfani da shi a matsayin hukunci ko hanyar gyaran hali ba.

Kungiyar ta bukaci kotunan ƙasar su riƙa bin ka’idojin doka da mutunta haƙƙin bil’adama, musamman a lokutan da ake yanke hukunci kan al’amuran da suka shafi ɗabi’a da al’ada.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.


Post a Comment

0 Comments