Bala Muhammad ya rattaba hannu kan dokar ƙirƙirar sabbin masarautu 13 a Bauchi.
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, ya amince da dokar da ta ƙirƙiri sabbin masarautu 13 a fadin jihar, domin faɗaɗa tsarin mulkin gargajiya da tabbatar da wakilci ga al’umma a matakai daban-daban.
Wannan mataki ya biyo bayan amincewar Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, wacce ta tattauna tare da nazartar rahoton kwamitin da gwamnan ya kafa a baya domin tantance buƙatun ƙirƙirar sabbin masarautu da gundumomi.
Gwamna Bala ya bayyana cewa ƙirƙirar sabbin masarautun na da nufin ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya, da ci gaban yankuna, tare da bai wa al’ummomi damar samun jagoranci na kusa da su.
An bayyana cewa sabbin masarautun za su taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsaro, ci gaban al’adu, da tabbatar da haɗin kai tsakanin jama’a da gwamnati.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
#Fitacciya #nacce #YancinFaɗa #Kano #’YanJarida #GwamnatinKano #YusufAbba #HakkokinDanAdam #FreePress #MediaFreedom #Najeriya #Democracy #YancinJarida #VoiceOfThePeople
0 Comments