Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.55 Don Binciken Albarkatun Ƙasa
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe kuɗi sama da Naira biliyan 2.55 domin gudanar da binciken kimiyyar ƙasa (Geoscience Survey) don gano albarkatun ƙasa da ke ɓoye a sassan jihar.
Gwamnatin ta bayyana cewa manufar binciken ita ce gano ma’adanai masu amfani kamar su zinariya, tagulla, Gwal, da sauran muhimman albarkatun da za su iya zama ginshiƙin tattalin arziƙin jihar da ƙasa baki ɗaya.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Hon. Sagir Musa Ahmad, ya ce wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Gwamna Malam Umar Namadi na bunƙasa tattalin arziƙi ta hanyar rage dogaro ga kuɗin gwamnati ta hanya ɗaya, da kuma samar da sabbin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.
Ya ƙara da cewa binciken zai kasance na kimiyya da fasaha, wanda zai ba da sahihan bayanai game da irin ma’adanan da ake da su a jihar da kuma yawan su, domin jan hankalin masu zuba jari daga cikin gida da wajen ƙasa.
Gwamnatin ta tabbatar da cewa za ta yi aiki kafada da kafada da masana da hukumomin ƙasa don tabbatar da cewa aikin ya gudana cikin gaskiya da bin ƙa’idar kare muhalli da amfanin jama’a.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments