(Sanate)
Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya ta bayyana aniyarta ta shiga tsakani domin sasanta rikicin da ke tsakanin Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur (PENGASSAN) da Dangote Refinery.
Rikicin dai ya ɓullo ne sakamakon takaddama kan tsarin aiki da wasu ma’aikata suka yi ƙorafi cewa kamfanin na tauye musu hakkoki, yayin da kamfanin ya kare kansa da cewa yana cikin tsarin sake fasalin ma’aikata ne domin inganta aiki da ingancin samar da man fetur.
Majalisar ta ce wannan rikici na iya yin illa ga manyan Masu Hannun jari da kamfanin Dangote, wanda ya zama ɗaya daga cikin muhimman ginshiƙan tattalin arziƙin Najeriya.
Wakilan majalisar karkashin jagorancin Hon. Tajudeen Abbas, sun amince da kafa wani kwamiti da zai shiga tsakanin ɓangarorin biyu, PENGASSAN da Dangote Refinery domin tabbatar da zaman lafiya da daidaiton alaƙar aiki.
Wasu mambobin majalisar sun kuma yi gargadin cewa irin wannan matsala na iya rage amincewar masu zuba jari na cikin gida da na waje, muddin ba a shawo kanta cikin adalci da gaskiya ba.
A gefe guda, majalisar ta jaddada muhimmancin kare haƙƙin ma’aikata tare da tabbatar da ci gaban masana’antu masu zaman kansu kamar Dangote Refinery, domin su ci gaba da taka rawa wajen samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
(Punch)
0 Comments