YANZU-YANZU: Ƴan sanda sun kama manyan dillalan miyagun ƙwayoyi uku a Jigawa, sun kwato magunguna fiye da 23,000

(Jigawa)

Ƴan sanda sun kama manyan dillalan miyagun ƙwayoyi uku a Jigawa, sun kwato magunguna fiye da 23,000!

Rundunar ƴan sanda ta jihar Jigawa ta cafke wasu manyan dillalan miyagun ƙwayoyi guda uku tare da kwato fiye da kwayoyi 23,000 a wani samame da ta kai a yankunan Garki, Fagam, da Maigatari.

Mai magana da yawun rundunar, ASP Lawan Shiisu, ya bayyana cewa an gano kwayoyin ne bayan samun sahihan bayanan leƙen asiri, inda jami’an tsaro suka gudanar da farmaki a wuraren da ake zargin ana boye miyagun ƙwayoyin.

Cikin abubuwan da aka kwato akwai Tramadol, Exol, D5, da Diazepam  waɗanda ake amfani da su wajen gurbata lafiya da tunanin matasa.

Rundunar ta tabbatar da cewa ana cigaba da bincike domin kamo sauran abokan harkar dillalan.

ASP Shiisu ya roƙi al’umma su ci gaba da ba da bayanan da za su taimaka domin dakile yaduwar miyagun ƙwayoyi a jihar da kasa baki ɗaya.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments