Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta sanar da dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta soma a fadin ƙasar.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, inda ya ce an dakatar da yajin aikin ne domin ba Gwamnatin Tarayya damar tattaunawa da aiwatar da bukatun malaman cikin wata guda.
ASUU ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan nazarin matsalolin da suka shafi:
Rashin biyan hakkokin malaman jami’a,
Bukatar ƙarin kuɗin gyaran jami’o’in gwamnati, da Jan kafa wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a baya.
Kungiyar ta gargadi cewa idan gwamnati ta kasa ɗaukar mataki cikin wannan lokaci, za ta sake komawa yajin aiki gaba ɗaya.
📢 “ASUU ba ta da niyyar cutar da ɗalibai, amma muna bukatar adalci da gaskiya wajen gyaran tsarin ilimi a ƙasar nan,” in ji Farfesa Piwuna.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments