ISWAP na shirin Kai Harr-Hare Jihohin Ondo da Kogi - DSS


Hukumar Tsaro ta Kasa, DSS, ta bayyana cewa kungiyar ta’addanci ta ISWAP na shirin kai hare-hare a wasu sassan jihohin Ondo da Kogi.

Rahoton da hukumar ta fitar ya nuna cewa an samu sahihin bayanan leƙen asiri da ke nuni da cewa ‘yan ta’addan na shirin kai harin da aka tsara sosai, musamman a Eriti Akoko, Oyin Akoko, da Owo, duk a Jihar Ondo.

DSS ta bukaci hukumomin tsaro su ƙara tsaurara matakan tsaro tare da yin sintiri a wuraren da ake zargin za a kai farmaki, domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Wannan gargaɗin ya zo ne bayan wani irin hari da aka kai a coci a garin Owo a shekarar 2022, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Hukumar ta kuma yi kira ga jama’a su kasance masu lura da abin da ke faruwa a muhallinsu, tare da gaggauta sanar da jami’an tsaro idan sun lura da wani abin da ba su yarda da shi ba.

Post a Comment

0 Comments