Yan sanda sun fara binciken jami’in da ya harbi mota a Delta

Yan sanda sun fara binciken jami’in da ya harbi mota a Delta

(officer)


Hukumar ‘yan sanda ta Jihar Delta ta tabbatar da fara bincike kan wani jami’in da aka gani yana harbi kan wata mota da ke tafiya a hanyar Okpanam, kusa da Toscana Hotel a garin Asaba.

Kakakin rundunar, SP Bright Edafe, ya bayyana cewa wannan aiki na jami’in abu ne “mai ban takaici kuma ba za a lamunta da shi ba.”

Edafe ya kara da cewa an gano jami’in, an tsare shi, kuma za a gurfanar da shi gaban kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Abaniwonda Olufemi, domin daukar matakin doka.

Rundunar ta jaddada cewa tana bin tsarin doka da ladabi, tare da tabbatar wa jama’a cewa babu wanda ya fi doka a Najeriya.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments