An sake samun takaddama tsakanin Akpabio da Natasha a majalisar dattawa kan kudirin zubar da ciki

An sake samun dan Ƙaramin rikici tsakanin Akpabio da Natasha a majalisar dattawa kan kudirin zubar da ciki

(Natasha And akpabio)

An samu ɗan takaddama a zaman majalisar dattawa a ranar Talata, lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar mazabar Kogi ta Tsakiya suka yi sabani yayin tattaunawa kan kudirin gyaran dokar aikata laifuka da ke neman tsananta hukunci ga masu taimakawa wajen zubar da ciki.

Kudirin, wanda Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, yana neman ƙara hukuncin daga shekaru uku zuwa shekaru goma a gidan yari, ba tare da zabin biyan tara ba. 

Sai dai wasu daga cikin sanatocin sun nuna damuwa cewa wannan matakin na iya hana likitoci yin aikin ceto a lokutan gaggawa inda rayuka ke cikin haɗari.

Bayan muhawara ta yi zafi, Akpabio ya dakatar da tattaunawar, ya kuma umurci kwamitin majalisar kan shari’a da doka da su sake nazarin kudirin cikin makonni biyu masu zuwa.

Sai dai bayan an dakatar da batun, Sanata Natasha ta nemi damar yin magana tana mai cewa kudirin ya shafi mata kai tsaye, amma Akpabio ya hana ta, yana mai cewa an rufe tattaunawar gaba ɗaya.

Sanata Adams Oshiomhole ya goyi bayan matakin Akpabio, yana cewa sake buɗe batun zai saba wa dokokin majalisar.

Bayan zaman, Natasha ta bayyana takaicinta bisa hana ta damar yin magana kan batu da ta ce ya shafi haƙƙin mata da lafiyarsu, tana mai cewa za ta bayar da gudunmawa lokacin da kwamitin zai sake nazarin kudirin.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.


(Dailynigerian Hausa)

Post a Comment

0 Comments