Yan bindiga sun kashe mutum biyu a harin da suka kai a Jos ta Kudu

Yan bindiga sun kashe mutum biyu a harin da suka kai a Jos ta Kudu.

(gun men)


Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a kauyen Daron da ke karamar hukumar Jos ta Kudu, jihar Plateau, inda suka kashe mutum biyu tare da raunata wasu da dama.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne da yammacin Litinin, inda suka bude wuta kan mazauna yankin ba tare da wani dalili ba, lamarin da ya haddasa firgici da gudun neman mafaka a tsakanin jama’a.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa, “Mun ji karar harbe-harbe da karfe 9 na dare, mutane suka fara gudu. Lokacin da komai ya lafa, an tarar da wasu mutane biyu sun mutu.”

Rundunar ‘yan sandan jihar Plateau ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an tura jami’ai zuwa yankin domin gudanar da bincike da kuma tabbatar da tsaro.

Lamarin ya sake tayar da hankalin jama’a a yankin, yayin da ake ci gaba da samun hare-haren ‘yan bindiga a wasu sassan jihar Plateau da ke fama da rikice-rikicen ƙabilanci da na manoma da makiyaya.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments