Yan Sanda Sun Gargadi Direbobi a Zamfara Kan Rufe Lambar Mota

Yan Sanda Sun Gargadi Direbobi a Zamfara Kan Rufe Lambar Mota.
(police officers)


Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta gargadi direbobi da masu mota da su guji rufe ko ɓoye lambar farantin motocinsu, musamman a cikin babban birnin jihar, Gusau.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba, yana mai cewa rufe ko ɓoye flate Number mota ya sabawa dokokin zirga-zirga na ƙasa.

Ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ibrahim Balarabe Maikaba, ya umurci jami’an tsaro su kama duk wani direba da aka samu da irin wannan laifi, tare da kwace motar har sai an tabbatar da ingancin takardunta.

Rundunar ta kuma roƙi jama’a da su taimaka wajen bayar da bayanai kan duk wanda ke amfani da mota da aka ɓoye ko rufe lambarta, domin kare tsaro da bin doka.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

(Tvc)

Post a Comment

0 Comments