Ɗan shekara 15 ya fada hannun ‘yan sanda bisa zargin fashi a Gombe

Ɗan shekara 15 ya fada hannun ‘yan sanda bisa zargin fashi a Gombe.
(police)

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wani matashi mai shekaru 15 da ake zargi da aikata jerin fashi a yankin Tudun Wada, Shamaki Quarters na birnin Gombe.

Mai magana da yawun rundunar, SP Mary Malum, ta tabbatar da cewa an kama matashin ne bayan samun korafe-korafen jama’a kan ayyukan fashi da makami da ke faruwa a unguwar.

Ta ce tuni ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, domin gano ko akwai wasu abokan aikinsa da ke da hannu a cikin laifin.

Rahotannin Fitacciya sun ce wanda ake zargin ya riga ya taba shiga hannun jami’an tsaro a baya saboda irin wannan laifi.

Fitacciya ta gano cewa rundunar ta yi kira ga iyaye da masu kula da yara su ɗauki nauyin tarbiyyar ‘ya’yansu, don kaucewa fadawa cikin miyagun halaye.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments