gazawar gwamnatin Tinubu na iya haifar da rashin amincewa da shugabanni a nan gaba.

Gazawar gwamnatin Tinubu na iya haifar da rashin amincewa da shugabanni a nan gaba.

(Shehu Sani)


Tsohon sanata kuma ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin bil’adama, Shehu Sani, ya bayyana cewa idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kasa cimma nasara wajen tafiyar da mulkinsa, hakan zai iya shafar makomar shugabannin da za su zo a nan gaba.

A cewar Shehu Sani, Najeriya na cikin wani mataki da ta ke buƙatar shugaba mai hangen nesa, wanda zai iya gyara tsarin tattalin arziƙi da zamantakewar al’umma.

Ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi, inda ya yi gargadin cewa gazawar gwamnatin Tinubu na iya haifar da rashin amincewa da shugabanni a nan gaba.

Shehu Sani ya ƙara da cewa, shugabanni su daina ɗaukar masu adawa a matsayin abokan gaba, domin a cewarsa, hakan yana jawo rikice-rikicen siyasa da rashin ci gaba a ƙasar.

Ya kuma bukaci gwamnatin Tinubu ta fifita cancanta da kwarewa wajen zaɓar mukamai, ba wai son rai da siyasa kawai ba.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.


Post a Comment

0 Comments