Bauchi ta sayi na’urorin zamani guda 13 don gano cutar tarin fuka (TB)

Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da cewa ta sayi sabbin na’urorin digital X-ray scanners guda 13, domin ƙara inganta gano cutar tarin fuka (TB) a fadin jihar.

(Bala Muhammad)

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Adamu Sambo, ne ya bayyana haka yayin kaddamar da na’urorin a Bauchi, inda ya ce sayen na’urorin ya zama wani Babban mataki wajen yaki da cutar a matakin farko.

Ya ce waɗannan na’urori masu ɗaukar hoto ta hanyar fasahar zamani za su taimaka wajen gano cutar cikin sauri, musamman a yankunan da ke da nisa da manyan cibiyoyin lafiya.

“Mun sayi waɗannan na’urori domin tabbatar da cewa duk wanda ke ɗauke da TB za a gano shi cikin lokaci, a kuma fara masa magani ba tare da jinkiri ba. Wannan zai taimaka wajen rage yaduwar cutar a tsakanin jama’a,” in ji Kwamishinan.

Rahotanni sun nuna cewa jimillar kudin sayen na’urorin ya kai tsakanin dala 150,000 zuwa dala miliyan 1.9, bisa bayanan da suka fito daga hukumomi daban-daban.

Ana sa ran na’urorin za su raba su zuwa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a sassan jihar domin su taimaka wajen gano masu cutar TB, musamman a yankunan karkara.

Cutar tarin fuka na daga cikin manyan matsalolin lafiya da ke addabar Najeriya, inda hukumar lafiya ta duniya (WHO) ke kiyasta cewa dubban mutane ke kamuwa da ita a kowace shekara, amma da dama ba a gano su da wuri ba.

Wannan mataki na gwamnatin Bauchi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara kira ga sauran jihohin ƙasar da su rungumi amfani da sabbin fasahohi wajen inganta tsarin gano da kuma magance cututtuka masu yaduwa.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments