An Zargi Matashi Mai Shekaru 17 Ya Cire Idon ‘Yar Uwarsa Don Yin Tsafi a Bauchi

An Zargi Matashi Mai Shekaru 17 Ya Cire Idon ‘Yar Uwarsa Don Yin Tsafi a Bauchi.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Auwalu Muhammad, ɗan shekaru 17, bisa zargin cewa ya Cire idanuwan ƙanwarsa don yin tsafi na neman kuɗi.

Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ƙauyen Wailo, da ke cikin ƙaramar hukumar Ganjuwa, ranar 17 ga watan Oktoba.

Rahotanni Fitacciya  sun nuna cewa matashin ya yaudari ƙanwar ta sa da ta biyo shi zuwa cikin daji, inda ya aikata wannan mummunan aiki.

An garzaya da yarinyar zuwa asibiti domin samun kulawa, sai dai likitoci sun tabbatar da cewa ta rasa Ganin ta na dindin din.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai bayyana shi da cewa “abin kunya ne, kuma nuna rashin ɗan adam.”

Ya ƙara da cewa, bayan binciken farko, an kama wasu mutum shida da ake zargin suna da hannu a cikin lamarin.

Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin dalilin da ya sa aka aikata wannan mugun aiki da kuma ko akwai wasu da ke bayan fage.

Fitacciya ta lura cewa irin waɗannan al’amura suna ƙara yawaita a wasu sassan ƙasar, abin da ke bukatar hukumomi da iyaye su ƙara sa ido wajen tarbiyya da tsaron yara.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.




Post a Comment

0 Comments