Wani rikici da ya samo asali daga soyayya ya haifar da mummunar musiba a unguwar Oja Gboro, Ilorin, jihar Kwara, inda saurayi mai shekara 25, Hammed Usman Tunde, ya rasa ransa bayan abokinsa, Gafar, mai shekara 21, ya soka masa wuƙa a kirji.
Shaidu sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wajen mai sayar da rake, bayan cece-kuce kan wata budurwa da dukkansu ke nema.
Rikicin ya ƙara zafi, har Gafar ya caka wa Tunde wuƙa, wanda hakan ya jawo masa mummunar rauni.
An garzaya da Tunde zuwa asibiti cikin hanzari, sai dai daga bisani likitoci suka tabbatar da cewa ya riga ya mutu.
Bayan faruwar lamarin, wanda ake zargi ya tsere, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da neman sa.
Iyalan marigayin sun roƙi gwamnati da hukumomin tsaro da su tabbatar da an kama wanda ya aikata kisan tare da kawo cikakken adalci.
0 Comments