Gwamna Bago Ga Jama’ar Jihar Neja: “Ku Kare Kanku, Ba Zan Biya Ƴan Ta’adda Fansa Ba”
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya gargadi jama’ar jihar da su tashi tsaye su kare kansu daga hare-haren ƴan ta’adda, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa biyan kudin fansa ko yin sulhu da masu sace mutane ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci al’ummomin Rijau da Magama, inda ya jajanta musu bisa hare-haren da aka kai a yankin Kontagora.
A cewarsa:
“Lokaci ya yi da jama’a za su ɗauki matakin kare kansu, domin biyan kudin fansa na ƙara ƙarfafa ayyukan garkuwa da mutane. Ni ba zan yi tattaunawa da ƴan ta’adda ba, kuma ba zan biya fansa ba. Da zarar ka fara biyan fansa, to kamar ka buɗe musu kasuwa ne.”
Bago ya ƙara da cewa halin da ake ciki yanzu ya zama tamkar yaƙi, wanda ke buƙatar haɗin kai da jajircewa daga kowa domin tunkarar barazanar tsaro.
“Doka ta ba mu haƙƙin kare kanmu da dukiyoyinmu. Ba mu da niyyar ja da baya dole mu fuskanci matsalar gaba ɗaya,”
in ji shi.
A cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka, Bago ya sanar da shirin daukar sabbin jami’ai 10,000 na Hadakar Tsaro (JTF) don taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a duk fadin jihar.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin jaridu, Aisha Wakaso, ta fitar, gwamnan ya kuma dakatar da dukkan ayyukan hakar ma’adinai a yankin Zone C, wanda ya haɗa da kananan hukumomi takwas; Magama, Kontagora, Rijau, Wushishi, Mariga, Borgu, Mashegu da Agwara.
Ya ce:
“Hakar ma’adinai ta zama ɗaya daga cikin manyan dalilan rashin tsaro a yankin. Abin mamaki ne yadda ma’adinai ke shiga dazuka ba tare da wata matsala ba, amma ƴan ta’adda ba sa taɓa su. Na umarci jami’an NSCDC da su kama duk wanda aka samu yana aikin hakar ma’adinai.”
Gwamnan ya tabbatar wa al’ummomin da abin ya shafa cewa gwamnati za ta tallafa musu ta hanyar ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu, magani ga waɗanda suka jikkata, da kuma sake farfaɗowa waɗanda suka rasa dukiyoyinsu da sana’o’insu.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments