Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 50 a hare-hare da dama a Borno da Yobe

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 50 a hare-hare da dama a Borno da Yobe.

(Nigerian troops)


Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 50 a hare-hare da dama a Borno da Yobe
Maiduguri  Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun samu nasarar fatattakar mayakan Boko Haram da ISWAP a jerin hare-hare da suka kai a wasu sassa na jihohin Borno da Yobe da safiyar Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025.

Rahotanni sun tabbatar da cewa daga ƙarfe 12:00 na dare zuwa 4:00 na safe, ‘yan ta’addan sun kai hari a yankunan Dikwa, Mafa, Gajibo da Katarko, inda dakarun suka tsaya ƙafafunsu suka yi musu ruwan wuta cikin ƙwarewa da jarumtaka.

Sojojin sun yi amfani da haɗin gwiwar jiragen yaki na Air Component Command na OPHK, waɗanda suka kai hare-haren sama cikin daidaito. Wannan ya taimaka wajen murkushe maharan tare da samun cikakken bayanin sirri daga na’urorin Intelligence, Surveillance and Reconnaissance (ISR).

A sakamakon haka, an kashe ‘yan ta’adda fiye da hamsin (50), tare da kwace bindigogi 38 na AK-47, manyan bindigogi 7 PKT, 5 RPG, 2 GPMG, da babban adadin harsasai. Sojojin kuma suna ci gaba da bin sawun wasu daga cikin maharan da suka tsere da raunuka.

Bincike ya nuna cewa maharan da suka kai hari a Dikwa da Gajibo sun fito ne daga yankin Cameroon, yayin da wadanda suka kai hari a Katarko suka fito daga Timbuktu Triangle, wanda aka fi sani da cibiyar mayakan Boko Haram.

Wasu daga cikin jarumai dakarun sun samu raunuka a fagen daga, amma suna cikin koshin lafiya. A wasu wurare kamar Mafa da Dikwa, an yi asarar motocin yaki da gine-gine sakamakon harin drone da RPG na ‘yan ta’addan.

Babban Hafsan Sojin Ƙasa ya yabawa dakarun bisa jarumtaka, jajircewa da sadaukarwar da suka nuna wajen kare martabar ƙasa da tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments