Gwamnatin Sakkwato Ta Ware Naira Biliyan 1 Domin Ciyar Da Mutane 34,000 Kullum

Ramadan: Gwamnatin Sakkwato Ta Ware Naira Biliyan 1 Domin Ciyar Da Mutane 34,000 Kullum.
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta amince da ware zunzurutun kuɗi har Naira biliyan ɗaya domin gudanar da shirin ciyarwa na musamman a cikin watan Ramadan mai zuwa.

Fitacciya ta rawaito cewa shirin zai mayar da hankali ne wajen samar da abinci ga mutane 34,000 a kowace rana a fadin jihar, a matsayin wani mataki na rage wa al'umma raɗaɗin tsadar rayuwa da kuma taimaka wa masu azumi.

Kwamishinan Harkokin Addini na jihar ne ya bayyana hakan, inda ya ce gwamnati ta samar da wannan tsari ne domin tabbatar da cewa marasa ƙarfi sun samu abincin buɗe baki cikin sauƙi. An tsara samar da wuraren ciyarwa a masallatai da sauran wuraren taruwar jama'a da aka zaɓa a duk faɗin ƙananan hukumomin jihar.

Gwamnatin ta bayyana cewa an riga an kammala shirye-shiryen samar da kayan abincin da za a yi amfani da su, sannan an kafa kwamitocin da za su sa ido domin tabbatar da cewa abincin ya isa ga mutanen da aka nufa.

Wannan mataki ya biyo bayan ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta, wanda ya sa gwamnatin jihar ganin dacewar ƙara faɗaɗa shirye-shiryen jin ƙai ga al'umma a lokacin wannan wata mai alfarma.

Domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu, ku biyo mu a shafinmu na Facebook:
👇

Post a Comment

0 Comments