Siyasar Kano: Alhaji Warkal Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar APC Ya Koma Kwankwasiyya
Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Hon. Aminu Abdullahi, wanda aka fi sani da Alhaji Warkal, ya sanar da ajiye mukaminsa tare da ficewa daga jam’iyyar baki ɗaya.
Fitacciya ta rawaito cewa, Alhaji Warkal ya bayyana hakan ne a cikin wasiƙar murabus ɗinsa da ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, 15 ga Fabrairu, 2026. Ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin ya koma tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
A cikin wasiƙar tasa, ya bayyana cewa dalilansa na sauya sheƙa sun ta’allaka ne da sauyin tafiyar siyasa, inda ya jaddada cewa a yanzu goyon bayansa ɗari bisa ɗari yana ga jagoran tafiyar Kwankwasiyya.
Hon. Aminu Abdullahi ya yi amfani da damar wajen nuna godiyarsa ga shugabannin jam’iyyar APC da suka ba shi damar yin aiki a matsayin mai taimaka musu, sannan ya gode musu kan haɗin kan da suka ba shi a tsawon lokacin da ya kwashe yana gudanar da ayyukansa a ƙarƙashin jam’iyyar.
Wannan sauya sheƙa na Alhaji Warkal, wanda na kusa ne da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, babban rashi ne ga jam’iyyar APC a Jihar Kano, la’akari da matsayinsa da kuma lokacin da abin ya faru yayin da ake fuskantar sabon sauyin siyasa a jihar.
Domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu, ku biyo mu a shafinmu na Facebook:
👇
0 Comments