Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, yana shirin kai ziyara Jihar Katsina a ranar Talata

(VP Kashim Shatima)

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, yana shirin kai ziyara Jihar Katsina a ranar Talata domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka da suka haɗa da sabuwar hanya a cikin garin Katsina, da kuma ƙaddamar da Expanded National MSME Clinic karo na tara, wanda gwamnatin jihar za ta karɓi baƙunci.

A yayin ziyarar, Mataimakin Shugaban Ƙasa zai kuma ƙaddamar da Katsina State Sustainable Platform for Agriculture, wata sabuwar manhaja ta zamani da ke amfani da fasahar dijital domin bunƙasa harkokin noma da ƙarfafa tattalin arzikin manoma a jihar.

Kwamishinan Ayyuka na Jihar Katsina, Alhaji Sani Magaji Ingawa, ya bayyana cewa titin da za a kaddamar yana da tsawon kilomita uku, kuma an gina shi da kuɗin da ya kai naira biliyan 1.9.

Ya ce aikin na daga cikin shirin sabunta birane (Urban Renewal Program) da gwamnatin Dikko Radda ke aiwatarwa, wanda ya ƙunshi faɗaɗa tituna, saka fitilun titi masu Anfani da hasken rana, da gyaran ababen more rayuwa a manyan garuruwa.

Haka kuma, Kwamishinan Noma, Farfesa Ahmad Bakori, tare da Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Kasuwanci ta Jiha, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, sun bayyana shirye-shiryen da hukumominsu suka tanada domin tarbar Mataimakin Shugaban Ƙasa.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Dakta Bala Salis Zango, ya ce ziyarar ta Shettima za ta zama wata shaida ta irin jajircewar gwamnatin Dikko Radda wajen samar da shugabanci mai ma’ana da ayyukan da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a.

#Katsina #Shettima #MSMEClinic #Noma #TattalinArziki #Fitacciya

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments