Babu Wani Yunkuri Na Juyin Mulki da Aka Samu A Najeriya - HQ

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu shafukan yanar gizo kan zargin shirye-shiryen juyin mulki a ƙasar.
(Army HQ)

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Janar Tukur Gusau, ya fitar, ya bayyana cewa rahoton da ake yadawa ba shi da tushe balle makama, inda ya ce wasu kafafen yada labarai ne suka ƙirƙiro batun bisa hujjar soke faretin Ranar ’Yancin Kai da kuma binciken da ake yi wa wasu jami’an soja.

“Rundunar sojin Najeriya na tabbatar da cewa labarin juyin mulki ƙarya ne baki ɗaya,”
 in ji Gusau. 

“An soke faretin ne kawai domin bai wa shugaban ƙasa damar halartar wani muhimmin taro a wajen ƙasa, da kuma mayar da hankali kan yaƙin da ake yi da ta’addanci da ‘yan fashin daji.”

Janar Gusau ya ƙara da cewa binciken da ake gudanarwa kan jami’ai 16 na rundunar ba sabon lamari ba ne, domin irin waɗannan bincike na faruwa a kai a kai domin tabbatar da ɗa’a da tsabtace ayyukan soja.

Ya ce an kafa kwamiti na musamman da zai gudanar da binciken, kuma za a sanar da sakamakon sa bayan kammala aikin.

A kwanakin baya, gwamnatin tarayya ta sanar da soke faretin Ranar ’Yancin Kai da aka saba gudanarwa a ranar 1 ga Oktoba, ba tare da bayyana cikakken dalili ba.

 Daga bisani rundunar soji ta tabbatar da tsare jami’anta 16 bisa zargin karya ƙa’idojin aiki da rashin ladabi.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments