Hadin Kai Ne Zai saka Mu Samu Abinci Mia Gina Jiki - Mata Gwamnan Zamfara

(Zamfara first lady)

Matar Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bayyana cewa haɗin kai tsakanin gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da al’umma shi ne hanya mafi inganci wajen tabbatar da samun abinci mai gina jiki ga kowa da kowa a jihar.

Hajiya Huriyya ta bayyana haka ne yayin wani taro da aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar, wanda ya mayar da hankali kan hanyoyin da za su inganta lafiyar al’umma ta hanyar samun abinci mai kyau da kuma rage matsalar rashin abinci mai gina jiki.

Ta ce ya zama dole a haɗa kai wajen wayar da kan jama’a, musamman mata da iyaye, kan muhimmancin cin abinci mai kyau ga lafiyar iyalai da ci gaban yara.

“Ba aikin gwamnati kaɗai ba ne samar da abinci mai gina jiki.

Dole ne mu haɗa hannu gaba ɗaya  daga gwamnati zuwa masu zaman kansu da al’umma domin tabbatar da cewa kowa yana da damar samun abinci mai kyau,” in ji ta.

Hajiya Huriyya ta kuma yabawa ƙoƙarin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki wajen ɗaukar matakai na inganta samar da abinci a cikin gida, musamman ta hanyar tallafawa manoma da ƙarfafa ayyukan noma.


Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments