Jama'a Sun Haɗa Kai Sun Hana 'Yan Bindiga Shiga Garinsu A Katsina



Al’ummar wasu ƙauyuka a Jihar Katsina sun nuna bajinta da jarunta bayan da suka haɗa kai wajen dakile harin da wasu miyagun ’yan bindiga suka yi niyyar kai wa garuruwansu.

Fitacciya Ta Rawaito cewa, mazauna yankin sun fito ne da makaman gargajiya tare da tashi tsaye wajen kare kansu, bayan da suka sami labarin tahowar maharan da ke ƙoƙarin shiga cikin garin domin yin garkuwa da mutane da kuma sace dukiyoyi.

Kamar yadda jaridar Aminiya ta wallafa, wannan yunƙuri na jama’a ya sanya ’yan bindigar ja da baya bayan da suka ga karsashi da kuma shirin ko-ta-kwana da mazauna yankin suka yi, lamarin da ya hana maharan cimma mugun nufinsu.

Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa wasu yankuna a jihar sun fara fuskantar matsin lamba daga ’yan bindiga, waɗanda har suke gindaya wa al’umma sharuddan biyan haraji ko kuma fuskantar hari.

Al’ummar yankin sun bayyana cewa sun gaji da zama cikin fargaba, don haka suka yanke shawarar ba za su sake barin miyagu su shigo garuruwansu ba tare da nuna tirjiya ba, yayin da suke kira ga gwamnati da ta ƙara tura jami’an tsaro domin taimaka musu.

Hukumomi dai suna ci gaba da kira ga jama'a da su riƙa kai rahoton duk wani motsi na ban-da-karya, amma wannan jarunta ta mazauna garin ta zama abin magana duba da yadda suka nuna cewa haɗin kai zai iya magance matsalolin tsaro.

Shin kuna ganin idan dukkan al’ummomin da ke fuskantar hare-hare suka haɗa kai irin haka, za a iya murƙushe matsalar ’yan bindiga a ƙasar nan?

Kuna iya bibiyar shafin Fitacciya Media a Facebook domin samun ingantattun labarai ta wannan mahadin: https://facebook.com/fitacciyamedia

Post a Comment

0 Comments