Sanata Abdul Ahmed Ningi, mai wakiltar shiyyar Bauchi ta Tsakiya a majalisar dattawa, ya soki takwarorin sa ’yan siyasa, inda ya bayyana cewa ba sa yi wa talakawan da suka zaɓe su adalci, wanda hakan ya janyo ƙasar ba ta tsinci kanta a inda ake buƙata ba.
Fitacciya Ta Rawaito cewa, Sanata Ningi ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da ya yi da wani gidan rediyon ƙasashen waje, inda ya nuna takaicin yadda ’yan siyasa ke nuna himma wajen neman ƙuri’a amma suke mantawa da talakawa da zarar sun hau mulki.
A cewar Sanatan, babban abin takaicin shi ne yadda ake ci gaba da kashe talakawa a sassan ƙasar nan, musamman a Arewacin Najeriya, amma a maimakon shugabanni su mayar da hankali wajen magance matsalar, sai suka sanya lamuran zaɓe da siyasar 2027 a gaba.
Sanata Ningi ya bayyana cewa yanayin da ake ciki a arewa a yanzu ya nuna kamar mutanen yankin ba su da shugabanni, duba da yadda rahotannin kashe-kashe ke fitowa a kullum ba tare da an ga an ɗauki kwararan matakai ba.
Haka zalika, ya bayyana cewa shi ya sa ya nemi majalisa da ta dakatar da dukkan wasu harkokin siyasa a jihohi takwas na Arewa da matsalar tsaro ta fi kamari, har sai an shawo kan matsalar zubar da jinin da ake yi.
Wannan jawabi na Sanata Ningi ya jawo hankalin jama'a da dama, inda wasu ke ganin cewa gaskiya ya faɗa, yayin da wasu kuma ke ganin hakan a matsayin wani salo na siyasa duba da irin takaddamar da ya taɓa samu da majalisar a baya.
Shin kuna goyon bayan kiran da Sanata Ningi ya yi na cewa a dakatar da siyasa a jihohi takwas na Arewa har sai an magance matsalar tsaro?
Kuna iya bibiyar shafin Fitacciya Media a Facebook domin samun ingantattun labarai ta wannan mahadin: https://facebook.com/fitacciyamedia
0 Comments