Shugaba Tinubu Ya Aike Da Sunayen Sabbin Ministoci Da Mataimakin Gwamnan CBN Zuwa Majalisa

Shugaba Tinubu Ya Aike Da Sunayen Sabbin Ministoci Da Mataimakin Gwamnan CBN Zuwa Majalisa


Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika da jerin sunayen wasu mutane da yake son naɗawa a matsayin ministoci da kuma mataimakin gwamnan babban bankin ƙasa (CBN) zuwa ga majalisar dattawa domin tantancewa da amincewa.

Fitacciya Ta Rawaito cewa, shugaban ya buƙaci majalisar ta tantance Yuguda a matsayin sabon mataimakin gwamnan bankin na CBN, a matsayin wani ɓangare na gyara da sake fasalin tattalin arzikin ƙasa.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa, wasiƙar wadda shugaban majalisar dattawa ya karanta, ta ƙunshi sunayen mutanen da aka zaɓa domin cike gurbi a ma'aikatun tarayya daban-daban da suka kasance babu ministoci.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin sake lale a cikin majalisar zartarwa domin tabbatar da cewa an samu ƙwararrun da za su tunkari matsalolin da ƙasa ke fuskanta.

Ana sa ran majalisar dattawa za ta sanya waɗannan sunaye a cikin jadawalin ayyukanta na mako mai zuwa domin fara aikin tantance su ɗaya bayan ɗaya kamar yadda tsarin mulki ya tanada.

Masu sharhi na ganin cewa naɗin Yuguda a matsayin mataimakin gwamnan CBN zai kawo sabon jini a fannin tafiyar da kudaden ƙasa, duba da irin gogewar da yake da ita a fannin kuɗi da tattalin arziki.

Shin kuna ganin waɗannan sabbin naɗe-naɗe da shugaba Tinubu ya yi za su iya kawo sauyi na gaggawa ga yanayin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu

Kuna iya bibiyar shafin Fitacciya Media a Facebook domin samun ingantattun labarai ta wannan mahadin: https://facebook.com/fitacciyamedia

Post a Comment

0 Comments