ASUU ta bayyawa Majalisar Dattawa manyan Dalilan Ta Na Tsunduma Yajin Aiki na Makkonni 2

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta bayyana wa Majalisar Dattawa dalilan da suka tilasta mata shiga cikin yajin aikin gargadi na makonni biyu, wanda yanzu haka ya shiga rana ta biyar.

A cewar kungiyar mallaman, babban dalilinta shi ne buƙatar gwamnati ta ƙara saka jari a jami’o’in ƙasar domin inganta binciken ilimi, gina ingantattun gine-gine, da kuma ɗaga matsayin albashin malamai, wanda ta ce shi ne mafi ƙasa a duk fadin Afirka.

Rahotanni Fitacciya  sun bayyana cewa yajin aikin da aka fara a ranar Litinin, 13 ga Oktoba, ya samo asali ne daga zargin cewa Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) na ƙoƙarin kwace wani ɓangare na filin Jami’ar Abuja.

Haka kuma, ASUU ta nuna rashin jin daɗin yadda Ma’aikatar Ilimi ta yanke shawarar raba biliyan 50 da aka ware wa jami’o’i da polytechnics da kwalejojin ilimi, wanda ta ce hakan zai rage tasirin kuɗin da jami’o’i ke buƙata.

Sai dai kungiyar ta yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bada biliyan 150 domin tallafa wa jami’o’i, da kuma hana kafa sabbin jami’o’in gwamnati har tsawon shekaru bakwai.

Yayin da zaman tattaunawa ke ci gaba, Majalisar Dattawa ta nemi bangarorin biyu da su nemi hanyar sulhu domin kada yajin aikin ya ƙara dagula al’amuran ilimi a Najeriya.

📢 Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments