Wasu barayin daji sun sake kai hari a wani ƙauye da ke cikin ƙaramar hukumar Kusada a Jihar Katsina, inda suka addabi mazauna yankin tare da yin barna.
Rahotanni daga majiyoyin Fitacciya sun tabbatar da cewa maharan sun afka garin ne da daddare, inda suka yi ta harbe-harbe domin tsoratar da jama’a, sannan suka kwace dukiyoyi da dabbobi daga hannun manoma.
Wani mazaunin yankin ya ce, “Muna cikin tashin hankali da fargaba. Barayin sun shigo ne da bindigogi, suka yi harbi, mutane suka gudu cikin daji.”
A halin yanzu, hukumomin tsaro suna ƙoƙarin gano sahihin adadin asarar da aka yi da kuma kama waɗanda suka aikata laifin.
Kakakin rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina, SP Sadiq Aliyu Abubakar, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun isa yankin, kuma ana cigaba da bincike.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments