Yan sanda sun kama mutane shida kan zargin Manyan Laifuka a jihar Kwara

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kwara ta tabbatar da kama muta ne shida (6) bisa zargin hannu a kashe wani mutum, tare da wasu laifuka da suka haɗa da haɗin baki da aikata manyan laifuka.
(File Copy: Kwara State Commissioner of Police, Mr Adekimi Ojo)

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Mr Adekimi Ojo, ya bayyana cewa, daga cikin waɗanda ake zargin akwai mutum uku da ake tuhuma da hannu a kashe Rafiu Akao, mai shekaru 34, wanda aka ce an kashe shi a ƙauyen Asunlere, yankin Oke-Oyi, Ilorin, a ranar 4 ga Nuwamba, 2024.

Rundunar ta ce an kama sauran mutum uku ne a wani samame na daban, bayan samun bayanan sirri da suka kai ga gano inda suke buya.

Kwamishinan ya ƙara da cewa bincike yana ci gaba, kuma da zarar an kammala, za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Rundunar ta sake nanata kudirinta na ganin cewa an tabbatar da tsaro da zaman lafiya a dukkan sassan jihar.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

(Punch)

Post a Comment

0 Comments