‘Yan sanda sun kama gungun masu satar mota da fashi da makami a Legas
Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Legas ta kama mutum hudu da ake zargi da satar mota da kuma masu fashi da makami, waɗanda suka dade suna addabar masu motoci a cikin da wajen jihar.
Mai magana da yawun rundunar, Abimbola Adebisi, ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, tana mai cewa jami’an rundunar sun kama su ne bayan binciken sirri (intelligence-led operation) da aka gudanar daga ranar 15 zuwa 17 ga Oktoba, 2025.
A cewar sanarwar, ɓarayin suna shiga motoci a matsayin fasinjoji, amma da zarar sun shiga hanya sai su fitar da bindiga su tilasta wa direba ya ba su motarsa.
Wadanda aka kama sun haɗa da:
Taiwo Alabi (42)
Ogedengbe Lowis (46)
Ighodalo Enato Francis (37)
Osaro Eghe Abiodun (34)
An kama su ne a mafakar su da ke Igando, Jihar Legas, inda aka kwato abubuwa daga hannunsu kamar irin su; bindiga kirar pump-action, Beretta pistol, harsasai 48 na 9mm, harsashi 46 na bindiga, adda, da kuma toyota Sienna, Lexus ES350 guda biyu da Toyota Corolla.
A cewar Adebisi, bincike ya nuna cewa sun shafe lokaci suna kai hare-hare a jihohin Ogun, Oyo, da Edo, inda suke yin amfani da dabara ɗaya ta shiga mota a matsayin fasinja sannan su yi fashi.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Olohundare Jimoh, ya yabawa jami’an da suka gudanar da kamen, yana mai tabbatarwa da jama’ar Legas cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da tsaro da zaman lafiya ta hanyar binciken kwarewa da kuma basira.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya Dan Samun ingantatu kuma tsaftatatun labarai.
0 Comments