Shehu Sani Ya Bukaci EFCC Ta Binciki Gwamnatin El-Rufai A kan yadda ya sarrafa kudin Jihar Kaduna.
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi kira ga Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) da ta gudanar da bincike kan yadda Nasir El-Rufai ya gudanar da mulkin Jihar Kaduna na tsawon shekaru takwas.
Fitacciya ta rawaito cewa Shehu Sani ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga rahoton kwamitin bincike na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, wanda ya zargi gwamnatin El-Rufai da bacewar wasu kudade masu yawa da suka kai Naira biliyan 423.
A cewar tsohon sanatan, ya dade yana fadin cewa gwamnatin El-Rufai ta bar babban rami na bashi da kuma zarge-zargen rashawa a jihar, don haka ya zama wajibi hukumomin yaki da rashawa su shiga maganar domin tabbatar da an kwato dukiyar talakawa.
Shehu Sani ya jaddada cewa binciken ya zama dole domin a nuna wa duniya cewa ba a ware wasu mutane a matsayin wadanda doka ba ta hau kansu ba. Ya ce al'ummar Jihar Kaduna na da hakkin sanin yadda aka kashe kudaden jihar da kuma dalilin da ya sa aka bar jihar cikin matsanancin bashi.
Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon Gwamna El-Rufai yake ci gaba da musanta zarge-zargen da kwamitin majalisar ya gabatar, inda yake ikirarin cewa duk ayyukan da ya yi sun bi tsari da kuma doka.
Hukumar EFCC dai ba ta riga ta fito ta bayyana matsayarta kan wannan kira ba, yayin da takaddama tsakanin tsofaffin abokan hamayyar biyu take kara daukar sabon salo.
Domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu, ku biyo mu a shafinmu na Facebook:
👇
https://www.facebook.com/fitacciyamedia
0 Comments