Jam’iyyar APC a Zangon Kataf Ta Goyi Bayan Tinubu Da Uba Sani

Jam’iyyar APC a Zangon Kataf Ta Goyi Bayan Tinubu Da Uba Sani.
Jam’iyyar APC reshen Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf da ke Jihar Kaduna, ta bayyana goyon bayanta ɗari bisa ɗari ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma Gwamna Uba Sani.

Fitacciya ta rawaito cewa shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki daga yankin sun bayyana wannan matsayar ne yayin wani taron tuntuɓa da aka gudanar a ranar Lahadi, 15 ga Fabrairu, 2026.

A yayin taron, mambobin jam'iyyar sun bayyana gamsuwarsu da irin ayyukan ci gaba da Gwamna Uba Sani yake aiwatarwa a fadin jihar, musamman ma yadda yake tafiyar da kowa ba tare da nuna bambanci ba, lamarin da ya ce ya taimaka wajen samar da zaman lafiya a Kudancin Kaduna.

Haka kuma, sun jaddada goyon bayansu ga manufofin Shugaba Bola Tinubu na gyara tattalin arziƙin ƙasa, inda suka bayyana cewa za su ci gaba da yi wa gwamnatin tarayya da ta jiha kyakkyawan fatan nasara har zuwa zaɓe mai zuwa na shekarar 2027.

Shugabannin jam’iyyar na Zangon Kataf sun yi kira ga magoya bayansu da su ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki ɗaya, sannan su yi watsi da duk wani yunƙuri na raba kan mambobin jam’iyyar a yankin.

Sun ƙara da cewa haɗin kan da ake da shi a yanzu shi ne zai ba jam’iyyar APC damar samun gagarumar nasara a kowane mataki na zaɓe a nan gaba.

Domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu, ku biyo mu a shafinmu na Facebook:
👇

Post a Comment

0 Comments