Rukunin Kamfanonin Dangote Ya Baje Kolin Shirin 'Vision 2030' A Baje-kolin Kaduna

Rukunin Kamfanonin Dangote Ya Baje Kolin Shirin 'Vision 2030' A Baje-kolin Kaduna
Rukunin kamfanonin Dangote ya gudanar da ranarsa ta musamman a wurin taron baje-kolin kasuwanci na ƙasa da ƙasa karo na 47 da ake gudanarwa a Kaduna, inda ya nuna aniyarsa ta cimma burin shirin "Vision 2030".

Fitacciya ta rawaito cewa taron, wanda aka gudanar ranar Lahadi, 15 ga Fabrairu, 2026, ya zama dandamali ga kamfanin na Dangote wajen bayyana shirye-shiryensa na dorewa da kuma yadda yake gudunmawa wajen haɓaka tattalin arziƙin Nijeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.

Wakilan kamfanin sun bayyana cewa shirin "Vision 2030" yana mayar da hankali ne wajen ƙarfafa masana'antu, samar da ayyukan yi, da kuma tabbatar da cewa Nijeriya ta dogara da kanta a fannonin buƙatun yau da kullum da suka haɗa da siminti, sukari, gishiri, da kuma man fetur.

A yayin taron na Kaduna, kamfanin ya baje kolin kayayyaki daban-daban da yake samarwa, inda ya samu yabo daga mahalarta taron da kuma shugabannin ɗakin kasuwanci na Kaduna (KADCCIMA) bisa yadda yake tallafawa baje-kolin shekara da shekaru.

Masu ziyara a rumfar kamfanin na Dangote sun sami damar fahimtar sabbin dabarun kasuwanci da kuma yadda kamfanin yake amfani da fasahar zamani wajen samar da kayayyaki masu inganci waɗanda za su iya gogayya a kasuwannin duniya.

Gudanar da wannan rana ta musamman ya ƙara fito da matsayin kamfanin na Dangote a matsayin jagora a fannin masana'antu, tare da jaddada aniyarsa ta ci gaba da zuba jari domin cigaban ƙasa.

Domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu, ku biyo mu a shafinmu na Facebook:
👇

Post a Comment

0 Comments