Hisbah Ta Kama Matasa 9 Bisa Zargin Shirya Bikin 'Bankwana Da Shaiɗan' Na shiga watan Azumi.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata shida da maza uku bisa zargin shirya wani taron casu na musamman da suka kira "Bankwana da Shaiɗan" a matsayin shirin fuskantar watan Azumin Ramadan.
Fitacciya ta rawaito cewa Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah na Jihar, Dakta Mujahid Aminuddeen, shi ne ya tabbatar da kamun matasan. Ya bayyana cewa taron, wanda aka yi wa lakabi da "Operation Ramadan Karim", ya saɓa wa tarbiyya da koyarwar addini da kuma dokokin Jihar Kano.
A cewar Dakta Mujahid, matasan sun shirya taron ne tare da gayyatar wasu fitattun mawaƙa waɗanda aka sani da yaɗa baɗala domin yin raƙashewa da sunan bankwana da Shaiɗan kafin a fara azumi. Ya jaddada cewa irin wannan dabi'a ba za ta lamunce a jihar ba domin cin mutunci ne ga watan Ramadan mai alfarma.
Hukumar ta bayyana cewa a halin yanzu tana ci gaba da gudanar da bincike a kan matasan, kuma da zaran an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci daidai da abin da suka aikata.
Daga ƙarshe, Dakta Mujahid ya yi kira ga iyaye da al'umma baki ɗaya da su ci gaba da sa ido kan zirga-zirgar yaransu, sannan su riƙa kai wa hukumar rahoton duk wani taro ko dabi'a da suka ga ta saɓa wa ka'idojin tarbiyya a yankunansu.
Domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu, ku biyo mu a shafinmu na Facebook:
👇
0 Comments