Dakarun sojin rundunar Operation Whirl Stroke sun samu gagarumar nasarar ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Kyado dake ƙaramar hukumar Ukum a Jihar Benue, bayan wani samame na musamman da aka kai domin fatattakar ɓatagari.
Fitacciya ta rawaito cewa, a cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Ahmad Zubairu ya fitar a ranar 16 ga watan Afrilun 2026, sojojin sun yi nasarar kuɓutar da Sylvester Micheal Ebuka da Chidinma Chikwentu cikin ƙoshin lafiya ba tare da sun samu wani rauni ba.
Rahoton ya nuna cewa an sace Ebuka ne tun a ranar 2 ga watan Afrilu, yayin da ita kuma Chikwentu aka yi garkuwa da ita a ranar 6 ga watan na Afrilu a lokuta daban-daban, inda sanarwar ta bayyana cewa nasarar ta samu ne sakamakon sahihan bayanan sirri da kuma tsananta matsin lamba da sojojin suka yi wa ƴan bindigar.
Bayanai sun tabbatar da cewa dakarun sojin sun mamaye maɓoyar masu garkuwar, lamarin da ya tilasta musu tserewa cikin daji tare da barin mutanen da suke tsare da su, inda kwamandan rundunar, Manjo Janar Moses Gara, ya jinjina wa sojojin bisa ƙwarewa da jajircewar da suka nuna wajen gudanar da aikin.
Haka kuma, Manjo Janar Moses Gara ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da irin waɗannan hare-hare domin kakkabe dukkanin wasu ɓatagari dake barazana ga zaman lafiyar al’umma, yayin da ya buƙaci jama’a da su ci gaba da ba su haɗin kai ta hanyar samar da sahihan bayanan sirri akan zirga-zirgar masu aikata laifuka.
Masu fashin baƙi na kallon cewa wannan nasara za ta ƙarfafa gwiwar mazauna yankin Ukum dake fama da ƙalubalen tsaro, duba da yadda haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da talakawa yake haifar da ɗa mai ido wajen daƙile ayyukan garkuwa da mutane da fashin daji.
A halin yanzu, dai an miƙa mutanen da aka ceto ga iyalansu bayan sun sami kulawar likitoci, yayin da dakarun rundunar Operation Whirl Stroke ke ci gaba da sintiri a yankunan domin tabbatar da cewa ɓatagarin ba su sake samun damar gudanar da ayyukansu ba a cikin mazauna yankin.
Kuna ganin cewa ƙarfafa kakkabe maɓoyar ƴan bindiga a dazuzzukan Jihar Benue zai isa ya kawo ƙarshen garkuwa da mutane, ko kuwa akwai buƙatar tattaunawa da jagororin yankunan domin samar da tsaro mai ɗorewa?
Domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu, ku biyo mu a shafinmu na Facebook:
👇
https://www.facebook.com/fitacciyamedia
0 Comments