Fitaccen mawaƙin yabon nan, Malam Bashir Dandago, ya girgiza fagen siyasa da fasaha ta hanyar sakin wata sabuwar waƙa mai cike da raddi da baƙin ciki, inda ya bayyana bacin ransa kan yadda wasu ƴan siyasa suka juya wa masoyansu baya bayan sun hau karagar mulki.
Fitacciya ta rawaito cewa, a cikin waƙar mai taken ”Kun cuce mu, kun yaudare mu, kun ƙware mu Allah ya isa” wadda take da tsawon mintuna 12 da sakan 28, Dandago ya fito fili ya nemi afuwar al’umma kan kiran da ya yi musu a baya na su zaɓi wasu shugabanni, inda ya bayyana cewa ya yi da na sanin barin aikin yabon Annabi da ya saba yi domin tsunduma cikin waƙar siyasa.
Rahoton ya nuna cewa mawaƙin ya yi fashin baƙi kan yadda suka jajirce wajen yawon kamfen a lungu da saƙo da kuma zama wakilai a rumfunan zaɓe, har ma da kare ƙuri’u lokacin da ake neman ƙwacewa, sai dai ya zargi shugabannin da nuna butulci ta hanyar watsar da ainihin masoyansu tare da rungumar waɗanda ya kira maƙiya bayan an raba madafun iko.
Bayanai sun tabbatar da cewa Malam Dandago ya yi gugar zana mai zafi ga wani babban jigo, inda ya yi zargin cewa mutumin ya nuna halin ko-in-kula tare da kai kayan al’umma ga maƙiyan mahaifinsa, sannan ya fito fili ya zargi jam’iyyar APC da zama silar jefa al’umma cikin mawuyacin hali da masifa sakamakon manufofinta.
Haka kuma, masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin cewa wannan waƙa ta Dandago za ta iya zama silar tada ƙura a fagen siyasar Arewa, duba da yadda mawaƙin yake da babban tasiri a wurin talakawa da kuma yadda saƙonnsa ya taɓo batun amana da butulci dake zama babban jigo a dambarwar siyasar yau.
Masu fashin baƙi na kallon cewa raddin Dandago wata alama ce dake nuna tsamin dangantaka tsakanin mawaƙan siyasa da shugabannin da suka taimaka wa, lamarin da ka iya shafar yadda kamfen ɗin zaɓen 2027 zai kasance, musamman idan mawaƙa masu faɗa a ji suka fara janye goyon bayansu ga jam’iyyu masu mulki.
A halin yanzu, dai waƙar ta fara yaɗuwa kamar wutar daji a kafafen sadarwa na zamani, inda jama’a ke fashin baƙi kan wa mawaƙin yake yi wa gugar zana, yayin da masoya Dandago ke ganin cewa ya yi daidai da ya fito ya faɗi gaskiya duba da yanayin da al’umma suke ciki na matsin rayuwa.
Kuna ganin cewa waƙar Bashir Dandago za ta iya sa ƴan siyasa su sake yin tunani kan yadda suke mu’amala da masoyansu bayan zaɓe, ko kuwa hakan ba zai sauya komai ba a tsarin siyasar Najeriya?
Domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu, ku biyo mu a shafinmu na Facebook:
👇
0 Comments