Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya tada ƙura a sararin siyasar jihar bayan da ya bayyana sunan Sanata Ahmed Aliyu Wadada a matsayin mutumin da yake sha’awar ya gaje shi bayan ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu a shekarar 2027.
Fitacciya ta rawaito cewa, a wani rahoton jaridar Vanguard na ranar 16 ga watan Afrilun 2026, Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da jiga-jigan siyasa, inda ya yaba wa ƙwarewa da kuma irin kishin ƙasa dake tattare da Sanata Wadada, wanda a halin yanzu yake wakiltar shiyyar yamma ta Jihar Nasarawa a majalisar dattawa.
Rahoton ya nuna cewa gwamnan ya jaddada cewa ko da yake akwai wasu masu neman takarar, amma yana ganin Wadada ne zai iya ɗora wa daga inda ya tsaya wajen bunƙasa masana’antu da samar da ayyukan yi a jihar, matakin da wasu ke gani a matsayin wani salo na nuna haɗin kai tsakanin jam’iyyar APC da SDP, duba da cewa Sanatan ya lashe zaɓensa ne a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar SDP.
Bayanai sun tabbatar da cewa wannan sanarwa ta janyo mahawara mai zafi a tsakanin mambobin jam’iyyar APC masu neman takarar, inda wasu ke ganin hakan a matsayin fifita bare fiye da ɗan gida, yayin da magoya bayan Wadada ke murnar cewa hakan zai kawo ƙarshen rarrabuwar kawunan ƴan siyasa a jihar domin samar da ci gaba mai ɗorewa ga al’ummar Nasarawa baki ɗaya.
Haka kuma, masu lura da al’amuran siyasa na ganin wannan mataki na Gwamna Sule a matsayin wani babban hangen nesa na samar da maslaha kafin zaɓen 2027, duba da yadda Sanata Wadada ke da babban tasiri a fadin jihar, wanda hakan zai iya sanya wasu ƴan takarar janye aniyarsu domin mara wa zaɓin gwamnan baya.
Masu fashin baƙi na kallon cewa ayyana magaji tun yanzu wani salo ne na gwamnan na tabbatar da cewa ya samu nutsuwar gudanar da ragowar ayyukansa na mulki ba tare da takun saƙar ƴan neman takara ya gurgunta masa tsare-tsarensa ba, kodayake hakan na iya fuskantar ƙalubale daga wasu jiga-jigan dake jin an yi musu ba daidai ba.
A halin yanzu, dai fagen siyasar Jihar Nasarawa ya sauya launi, inda aka fara tattaunawa kan yadda za a fuskanci wannan sabon lissafi, yayin da ake jiran ganin matakin da Sanata Wadada zai ɗauka na komawa jam’iyyar APC ko kuma ci gaba da zama a SDP domin gudanar da takararsa a nan gaba.
Kuna ganin cewa ayyana Sanata Aliyu Wadada a matsayin magaji zai taimaka wa Gwamna Sule wajen samar da zaman lafiya a siyasar Jihar Nasarawa, ko kuwa hakan zai ƙara rura wutar rikicin cikin gida ne a jam’iyyar APC?
Domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu, ku biyo mu a shafinmu na Facebook:
👇
0 Comments