Al’ummar Shanono a Kano sun koka kan yawaitar hare-haren ‘yan bindiga

(Shanono)


Al’ummar ƙaramar hukumar Shanono da ke Jihar Kano sun bayyana tsananin damuwarsu kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ƙaruwa a yankin, lamarin da ke jefa rayukan mutane cikin tashin hankali da fargaba.

Wani daga cikin shugabannin al’umma, Yahaya Umar Bagobiri, wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro na yankin, ya bayyana cewa hare-haren sun fi kamari a unguwannin Faruruwa, Kuraku, Goron Dutse da Tsaure, inda ‘yan bindiga ke zuwa dauke da makamai masu nauyi suna satar dabbobi da garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Bagobiri ya bayyana cewa tun daga shekarar 2022 ake fama da wannan matsala, inda ake yawan samun kashe-kashe, sata, da kone-konen gidaje da gonaki.

“Mutane suna rayuwa cikin fargaba. Kowa yana tsoron fita gona ko tafiya da dare. Idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba, wannan matsala za ta ƙara ta’azzara,” in ji shi.

Ya roƙi gwamnatin tarayya da ta jiha da su ƙara yawan jami’an tsaro a yankin, su samar da kayan aiki na zamani, tare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro domin magance wannan barazana.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments