Gwamnatin Tarayya ta ɗauki mataki mai tsauri kan wasu jami’an Hukumar Shige da Fice ta ƙasa (Nigeria Immigration Service – NIS) bisa samun su da laifuka daban-daban da suka haɗa da satar kaya, yin hulɗa da masu aikata laifuka, da kuma aikata wasu ayyukan da suka saba da doka da ka’idojin aiki.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Akinsola Akinlabi, ya fitar, hukumar ta Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board ta gudanar da bincike kan jami’an 31, inda ta yanke hukunci bisa sakamakon rahoton da aka gabatar.
Daga cikin matakan da aka ɗauka sun haɗa da:
Jami’ai 8 an kore su daga aiki saboda manyan laifuka;
Jami’ai 5 an tilasta musu yin Ritaya;
Jami’ai 8 kuma an sauke su daga mukamansu;
Sauran jami’ai biyu ƙanana kuma an kore su saboda aikata laifuka irin su satar kaya da riƙe makami ba bisa ƙa’ida ba.
Akinlabi ya bayyana cewa gwamnati da hukumar ba za su lamunci karya doka da rashin gaskiya a cikin jami’an tsaro ba, yana mai cewa za a ci gaba da ɗaukar irin waɗannan matakai domin tabbatar da gaskiya da tsafta a aikin gwamnati.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
#Fitacciya #nacce #YancinFaɗa #Kano #’YanJarida #GwamnatinKano #YusufAbba #HakkokinDanAdam #FreePress #MediaFreedom #Najeriya #Democracy
0 Comments