Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ziyarci garin Essa da ke cikin ƙaramar hukumar Katcha, domin jajantawa al’ummar yankin bisa mummunar fashewar tankar mai da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama da kuma jikkatar wasu.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Bologi Ibrahim, ya fitar.
A yayin ziyarar, Gwamna Bago ya gargadi jama’a da su guji zuwa wajen tankar mai da ta faɗi domin dibar man fetur, yana mai jaddada cewa wannan aiki ne mai haɗari kuma babban laifi da gwamnati ba za ta lamunta da shi ba.
Gwamnan ya kuma sanar da tallafin naira miliyan ɗaya (₦1,000,000) ga kowace iyali da ta rasa ɗan uwa a hatsarin, tare da naira dubu dari biyar (₦500,000) ga waɗanda suka jikkata.
A ƙarshe, Bago ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tare da Kamfanin Dangote za su fara aikin gyaran hanyar Mokwa zuwa Lambata, da kuma gina asibiti a garin Essa domin rage raɗaɗin al’umma.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments