Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya rantsar da sabbin kwamishinoni uku tare da sakatarori na dindindin takwas domin kara karfafa aikin gwamnati da inganta gudanarwa a jihar.
A yayin bikin rantsuwar da aka gudanar a ofishin gwamnatin jihar, Gwamna Radda ya bukaci sabbin jami’an da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, adalci, da tsoron Allah, yana mai jaddada cewa mukaman da aka ba su babban amanar da za su bayar da hisabi a kanta.
Ya bayyana cewa wannan sabon rantsuwar wani bangare ne na kimantawar rabin wa’adin mulkinsa, domin sake duba nasarorin da aka cimma da kuma gyara inda ake bukata.
Gwamnan ya yaba da kwazon da sabbin kwamishinonin suka nuna a fannoni daban-daban, inda ya ce:
Hon. Yusuf Suleiman Jibia, gogaggen dan siyasa wanda ya rike mukamai daban-daban a baya.
Hajiya Aisha Aminu, ta taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa matasa da mata a hukumarta ta KASEDA, abin da ya tabbatar da kudirin gwamnatin Radda na baiwa mata dama.
Engr. Dr. Sirajo Yusuf Abukur, ya samu yabo saboda jajircewa da aiki tukuru wajen gina hanyoyi a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar.
Haka kuma, Gwamna Radda ya ce nadin sabbin sakatarorin dindindin na nufin kara karfafa ingancin ma’aikata da samar da tsarin aiki na gaskiya da kwarewa.
Ya gargade su da cewa kada su yi amfani da mukamansu wajen zalunci ko nuna bambanci, yana mai cewa:
“Ku karanta rantsuwar da kuka dauka a gida. Wannan amana ce daga Allah, kuma kowa zai bayar da hisabi.”
Ya kara da cewa duk wanda ya aikata kuskure zai fuskanci hukunci, domin gwamnatinsa ba za ta lamunci rashin gaskiya ba.
A karshe, Gwamna Radda ya taya sabbin jami’an murna, ya kuma tunatar da su cewa mukamansu ba mallakar kowa bane, illa na mutanen Jihar Katsina da suke wakilta.
“Abin da za ku yi a ofis ku yi shi don al’ummar Katsina, ba don ni ba,” in ji Gwamna Radda.
An kammala taron da addu’a domin neman albarka da nasara wajen gudanar da sabbin ayyukan gwamnati.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments