YANZU - YANZU: me Wushirya ya Fasa Auren Yar Guda

Fitaccen Jarumin TikTok, Ashir Idris, wanda aka fi sani da Mai Wushirya, ya bayyana cewa ba shi da niyyar auren abokiyar wasansa Yar Guda, duk da yadda ake yada labarin cewa zai aure ta.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mai Wushirya ya ce tsoro ne ya sanya shi amincewa a gaban kotu cewa zai aure ta, amma a zahiri babu wani shirin aure tsakaninsu.

“Ni ba na son yin auren, haka ma Yar Guda ba ta da niyya. Na amince ne saboda tsoro da yanayin da ake ciki a lokacin,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa ba shi da hannu a taron kuɗin da wasu ke yi don tallafa musu da aure, yana mai roƙon a ba da kuɗin ga gidan marayu domin taimaka wa marasa galihu.

Mai Wushirya ya ce sun fahimci kuskuren da suka aikata, tare da neman afuwar jama’a saboda yadda lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

A baya dai, Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin wallafa bidiyo da ya saba da al’ada da tarbiyyar Hausawa, wanda ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments