Akwai Yiwuwar Gwamnati Ta Fasa Yiwa Wasu Afuwa daga Cikin Jerin Sunayen Da Aka saki Tun Farko

(shugaba Bola Ahmed Tunibu)


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na fuskantar matsin lamba daga jama’a da hukumomin tsaro bayan bayyana jerin sunayen wasu da ake shirin yi musu afuwa daurin da ake musu, ciki har da waɗanda ake zargi da manyan laifuka.

Rahotanni sun nuna cewa hukumomi da kungiyoyin kare hakkin bil adama sun nuna damuwa kan yadda sakin wasu daga cikin mutanen zai iya kawo tsaiko akan yaki da cin hanci da rashawa da kuma rashin tsaro a ƙasa.

Babban Lauyan Tarayya, Prince Lateef Fagbemi (SAN), ya bayyana cewa jerin sunayen da ake magana a kai ba a kammala tantance su ba, kuma gwamnati na duba yiwuwar cire sunayen da suka tayar da ya musi da husuma daga jerin kafin karshe.

Jaridar Punch ta rawaito cewa cikin jerin akwai wasu shahararrun fursunoni da aka yanke musu hukunci kan laifukan kisan kai, sata, da laifukan ta’addanci.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, manufar gafarar ita ce ta ba wa masu nadama dama, amma ta jaddada cewa ba za a bari a yi amfani da tsarin wajen kare manyan masu laifi ba.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments