Majalisar Dattawa ta shiga tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya kan rikicin yajin aiki


Majalisar Dattawa ta shiga tsakani domin kawo karshen rikicin da ke tsakanin ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, wato ASUU, da Gwamnatin Tarayya, biyo bayan dakatarwar aiki da ƙungiyar ta fara.

Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin jami’o’i da hukumar TETFund, Sanata Muntari Dan dutse, ya bayyana haka bayan wani muhimmin taro da aka gudanar a Abuja, inda ya ce Majalisar Dattawa tana ƙoƙarin tabbatar da an samu fahimtar juna tsakanin ɓangarorin biyu.

“Ba mu goyon bayan yajin aiki, kuma ba ma goyon bayan barazana daga kowanne ɓangare. Muna son ganin jami’o’inmu suna aiki cikin kwanciyar hankali, don ingancin ilimi a ƙasar nan,” in ji Dandutse.

Ya ƙara da cewa majalisar za ta mika matsalolin da ASUU ta gabatar ga Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) domin tattaunawa da nemo hanyar da ta dace wajen warware su.

A nasa bangaren, mataimakin shugaban ASUU, Farfesa Christopher Piwuna, ya jaddada cewa dalilan yajin aikin sun haɗa da:

Bukatar ƙarin kuɗi domin inganta jami’o’i,
Matsalolin albashi da yanayin aiki,
Da kuma batun ‘yancin gudanar da harkokin jami’o’i ba tare da tsoma baki ba.

Shi kuwa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya tabbatar da cewa za a yi duk mai yiwuwa domin ganin an kawo ƙarshen rikicin cikin gaggawa, don ba wa ɗalibai damar komawa makaranta cikin natsuwa.

Majalisar ta kuma yi kira ga ASUU da gwamnati da su ci gaba da tattaunawa cikin hikima, maimakon komawa ga yajin aiki wanda ke janyo cikas ga tsarin ilimi a ƙasar.

✍️ Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments