Ankama Wani matashi Bisa Zargin Kashe abokin Sa A bauchi wajen neman Kudin Aure macce ta 3

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Mamuda Zakari Yau, mai shekaru 30, bisa zargin kashe abokinsa Basiru Mohammed mai shekaru 25, domin satar mashin da yake haya da nufin samun kuɗin aure na mace ta uku.
Lamarin ya faru ne a unguwar Dakta Sulaiman Adamu da ke cikin birnin Bauchi, a ranar Alhamis, 16 ga Oktoba 2025, lokacin da wanda ake zargi ya cakka wa marigayin wuƙa yayin da yake ƙoƙarin sace mashin ɗin kirar Bajaj Boxer.

Bayan faruwar lamarin, jama’a suka cafke wanda ake zargi yayin da yake ƙoƙarin gudu, kuma Basiru Mohammed ya rasu a asibitin ATBUTH Bauchi sakamakon raunukan da ya samu.

A yayin bincike, Mamuda Zakari ya amsa cewa ya aikata laifin ne domin samun kuɗin auren mata ta 3.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin a miƙa wanda ake zargin zuwa SCID Bauchi domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a kotu.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments