GA MANYAN DALILAI DA YA KAMATA MAIGIRMA SHUGABAN KASA BOLA AHMED TINUBU YA UMURCI MINISTAN SHARI'AH KUMA BABBAN LAUYAN GWAMNATIN TARAYYA YA JANYE TUHUMAR DA AKE YIWA DCP ABBA KYARI DON AMFANIN TSARON KASA
Wanda ya rubuta Babban Lauya mai kare hakkin bil'adama Barr. Hamza Nuhu Dantani
J!ni yana kwarara a Nigeria daga yankin Arewa zuwa Kudu, daga jihar Zamfara zuwa Plateau, daga Jihar Kwara zuwa Borno, abin tausayi ne da yake faruwa, ‘Yan bindiga a kan babura suna mamaye garuruwan al’umma, suna garkuwa da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, suna ka$he manoma, suna garkuwa da mamaye wasu kananan hukumomin, ga rikicin B0k0 Har@m, tashin hankali da tsoro a kullun yana kara mamaye zukatan al'ummah
’Yan fashi da makami da B0k0 Har@m, da masu tada kayar baya, da aikata munanan laifuka sun zama wani bangare na rayuwar yau da kullum a cikin al’ummar da ta kasance al’umma mai alfahari da 'yancinta, abin tambaya shine; wai shin ina kwararrun jaruman tsaro wadanda suke bamu kariya?
Sunan wani jarumin dan sanda DCP Abba Kyari ya karade kowani lungu da sako na Nigeria saboda tsananin jaruntarsa da kwarewarsa a bangaren yaki da masu aikata miyagun laifuka, har sai da aka kai lokacin da 'yan ta'adda sun fara guduwa da kafafunsu daga Nigeria saboda tsoron Abba Kyari da rundinarsa, amma yau an wayi gari yana tsare a kurkuku a daidai lokacin da Nigeria da 'yan Nigeria suke matukar bukatarsa, wanda fashinsa ya taba tsaron Kasa sosai
YA BAR TARIHI NA HIDIMA DA JARUNTAR DA YA YIWA TSARON KASA
Kafin a kulla sharri da makirci a tsare DCP Abba Kyari a kurkuku, ba kawai shi kwararren jami'in dan sanda bane, sunansa ya shiga kundin bajintar tsaro na Kasa, shine jami'in tsaron da yafi kowa samun lambar yabo a tarihin Nigeria, saboda kokarinsa na fada da miyagun laifuka, ta yanda ya karya kashin gadon bayan 'yan ta'addan da ake ganin sun gagara
DCP Abba Kyari ya jagoranci rundinar IRT suka wargaza shirin mafiya hatsarin 'yan ta'adda da suka cutar da Nigeria da 'yan Nigeria zuwa kowani kusurwa na Kasarnan, tun daga kama hamshakin attajirin nan mai garkuwa da mutane Evans har zuwa kamo kwamandan B0k0 Har@m Umar Abdulmalik, da wargaza kungiyar ‘yan fashin bankin Offa, da ceto mutanen da akayi garkuwa da su wanda ba adadi, da kama rundinar 'yan B0k0 Har@m masu tsara harin bama-bamai har aka wayi gari b0mb ya dena tashi, DCP Kyari ya yi kaurin suna a matsayin jami'in tsaron da zai iya zuwa inda wasu jami'an tsaro ke tsoron zuwa
DCP Abba Kyari ya kaddamar da samame a lokuta dabam-dabam, ya kakkabe ‘yan ta’adda, kungiyoyin ta’addanci, da dillalan makamai da suka addabi ‘yan Nigeria tsawon shekaru, Abba Kyari da yaransa sun dauki nauyin kama wasu masu garkuwa da mutane sama da 300, da kwato daruruwan bindigogi kirar AK-47, da wargaza hanyoyin sadarwan ‘yan ta’adda da ke aiki a yankin Arewa da Kudancin Nigeria
DCP Abba Kyari ne ya kama ‘yan ta’addan B0k0 Har@m ashirin da biyu (22) wanda suka yi garkuwa da ’yan matan makarantar Chibok a shekarar 2014 da kuma daukar nauyin kai hare-haren kunar bakin wake da dama, da kuma yi wa Jami’an tsaro kwanton bauna a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa wanda yaja hankalin Kasashen duniya, amma abin takaici mutum 7 da ke da hannu a sace ‘yan matan makarantar Chibok sun tsere a gidan yarin Kuje yayin harin ta’addancin da aka kai a watan Yulin 2022
Ba abin mamaki ba ne cewa DCP Abba Kyari ya zama dan sandan da aka fi bawa lambar yabo a tarihin Nigeria, domin ya samu lambobin yabo daga Shugabannin kasa, Gwamnoni, da kungiyoyin kasa da kasa baki daya, ciki har da lambar yabo ta shugaban kasa na jajircewa a shekarar 2016, da lambar yabo na jami'in da yafi kowani jami'in tsaro a Nahiyar Afirka kwarewa a bincike a 2018, da lambar yabo ta Majalisar Dokoki na Kasa kan kyakkyawan hidima ga Kasa da yayi
Wadannan lambobin yabo da ya samu ba alluna bane ko kayan ado ba; suna wakiltar tarihin sadaukar da kai, jajircewa, da ceton rayukan 'yan Nigeria marassa adadi da DCP Abba Kyari yayi
KASARMU (NIGERIA) TANA BUKATAR JARUMINTA
Tun bayan tsare Abba Kyari a shekarar 2022, al'amuran tsaron Nigeria sun tabarbare sosai, 'Yan fashi da ta'addanci sun mamaye sabbin yankuna, a jihar Kwara wasu ‘yan fashi da makami na kai wa al’umma hari, a jihar Filato kuma wasu gungun ‘yan bindiga ne ke hallaka mutanen kauyuka, a Borno B0k0 Har@m da l$WAP na ci gaba da kai hare-hare, a Zamfara kungiyoyin 'yan bindiga mai ban tsoro suna ta kunno kai suna karbar haraji, suna mulkin 'yan kasa marassa galihu
Kasa na bukatar sakamako ba uzuri ba, idan aka zo ga sakamako ayyukan da DCP Abba Kyari yayi domin ya tsare Kasarnan a zahiri suke, rashinsa ya cutar da tsaron Kasar gabaki daya a daidai lokacin da kwarjini a tsakanin jami’an tsaro ke kara tabarbarewa kuma masu aikata laifuka ke kara himma, bai kamata Nigeria ta cigaba da ajiye daya daga cikin jami'an tsaronta masu hazaka a Kurkuku ba, a lokacin da laifuka ke kokarin cinye Kasa
BATUN ADALCI, HAKKIN DAN ADAM, DA FIFITA BUKATAR KASA AKAN KOMA
A matsayina na mai fafutukar kare hakkin dan Adam, na yi imani da bin tsarin doka da shari'ah tsantsa, duk wanda ake tuhuma da aikata wani laifi ciki har da DCP Abba Kyari, to ya cancanci a bi ka'ida
Duk da haka, bai kamata tsarin shari'ah na adalci yana tafiyar hawainiya ba, An shafe shekaru ana shari’ar Abba Kyari ba tare da an kammala shari’ar ba, yayin da ‘yan Nigeria a kullun suna rasa rayukansu a hannun 'yan ta'adda
Abin tambaya anan shine shin ya kamata a tsarin doka hazikin mutum irin Abba Kyari wanda Kasa ke amfana da kokarinsa a kyaleshi a kurkuku a lokacin da Kasar ke tsananin bukatarsa?
Wannan shine babban dalilin da yasa nake kira ga Maigirma Shugaban Kasar Nigeria ya fifita bukatar Nigeria akan komai, ya umarci Ministan shari'ah kuma Babban Lauyan Gwamnatin Nigeria ya janye ko ya dakatar da tuhumar da ake yiwa DCP Abba Kyari bisa kundin dokar Constitution sashi na 174 (C). A fitar dashi daga kurkuku ya dawo bakin aiki, a bashi wani aiki na musamman bangaren yaki da masu garkuwa da mutane a fadin tarayyar Nigeria ko a jihohin da aka fi fama da matsalar garkuwa da mutane
Sashin dokar Constitution na 174 da aka ambata a sama ya tanadi cewa yayin aiwatar da ikonsa, Babban Lauyan Gwamnatin Nigeria zai kula da bukatun jama'a da dai sauransu akan wanda ake zargi da aikata wani laifi, don haka a ra’ayina, wannan shari'ah na Abba Kyari ya cancanci a dubashi domin yana amfanar jama’ar Kasa ne, a janye karar da ake yiwa DCP Abba Kyari.
Akwai shari'ar da Kotu tayi akan case da ya gudana na OKORODUDU v. FRN & ORS (2015) LPELR-26029 (CA) cewa amfani da wannan ikon da dokar Kasa ta bawa Babban Lauyan Gwamnatin tarayya babu wani mutum har da Kotu da yake da ikon dakatar da ikon, za'a yi amfani da ikon ne a dawo da DCP Abba Kyari don tabbatar da tsaron Kasar, kamar yadda manyan Kasashe ke tunawa da manyan hafsoshin Sojojinsu da sukayi ritaya a lokutan yaki ta dawo dasu aiki, to ya kamata Nigeria ta tuna da jarumanta a wannan lokacin na rashin tsaro da ba a taba ganin irinsa ba
WANI MUTUM YA YI LOKACI KAMAR HAKA
Daga cikin tsarin dabi'ah ko hali na Jagora/Shugaba shine yayi kokarin sanin masu hazaka a cikin Kasa musamman a lokacin da Kasarsa ke da bukata, cigaba da tsare hazikin dan sanda irin DCP Abba Kyari a wannan lokacin da Nigeria ke bukatarsa kamar misalin ajiye shahararren dan kwallo na duniya Messi akan benci ne a lokacin da aka ci kulub dinsa wasa uku da babu kafin a hura tashi
A wannan lokacin da kungiyoyi masu aikata miyagun laifuka ke kara yaduwa kamar wutar daji, muna bukatar kwararren jami'in tsaro DCP Abba Kyari wanda ya fahimci yanayin Kasa, ya gina hanyoyin neman bayanan sirri na 'yan ta'adda a duk inda suke, ba sai ance wa kowa DCP Abba Kyari ya cancanta ba, duk abinda yayi na jarunta gasu nan ana ganinsu a zahiri
KIRA ZUWA GA MAIGIRMA SHUGABAN KASA
Maigirma Shugaban Tarayyar Nigeria ya yi alkawarin kawar da matsalar tsaro gaba daya domin a samu zaman lafiya, hakan ba zai yiwu ba har sai yayi amfani da kwararrun jami'an tsaro wadanda aikinsu ya tabbatar da jaruntarsu, sakin DCP Abba Kyari domin fifita bukatar Kasa ba wai alfarma bane, bukatace ta gaggawa ta kama domin amfanar Kasa, sakin Abba Kyari a wannan lokaci zai sa a fahimci Shugaban Kasa ya fifita darajar Nigeria akan kowace irin bukata
A matsayina na mai fafutukar kare hakkin dan adam, na yi imani da bin bahasi na ka'ida, amma duk da haka ina ganin cewa Kubutar da Kasarnan daga matsalar tsaro ta kowace irin hanya shine mataki na farko, Idan har tsaronmu ya ci gaba da durkushewa to zai shafi kowa da komai
A KARSHE: SABODA MAFI GIRMAN ALHERI GA AL'UMMA
DCP Abba Kyari ba ma'asumi bane, yana da nasa ajizancin, amma DCP Abba Kyari dan kishin kasa ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa a lokuta da dama don ya kare mu. Shekaru da dama da ya yi yana hidima wa Kasa ta hanyar sadaukarwa, abinda ya yiwa Kasa na alheri ya zarce zargin da ake masa a gaban kotu
A irin wannan lokaci, al'ummar Kasa haduwa suke guri guda ba wai su yi watsi da masu kokarin cikinsu ba, ba shakka Allah Ya albarkaci Nigeria da DCP Abba Kyari saboda lokaci na tabarbarewan tsaro irin wannan da ake fuskanta, yakamata shugaban kasa ya dawo da shi bakin aiki saboda duk wani dan Nigeria mai son yayi barci idanunsa biyu a rufe.
Rubutawa Barr Hamza Nuhu Dantani, Esq.
Lauyan Kundin Tsarin Mulki da Mai fafutukar kare hakkin bil'adama
16/10/2025
Muna fatan Allah Ya tabbatar mana da tsaro da zaman lafiya a Kasarmu Nigeria
0 Comments