Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wani Da Ake Zargi Da Laifin Kisa A Benue

(police officer)

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Benue ta tabbatar da mutuwar wani da ake zargi da aikata laifin kisa mai suna Saater Aii, wanda ake zargin ya kashe wani kwamandan mafarauta, Aondoakaa Yayol, a garin Wannune, karamar hukumar Tarka ta jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa Saater Aii ya kuma kashe matar yayansa mai suna Kashimana Yayol tun a ranar 11 ga Fabrairu, 2023.

A ranar Asabar, 18 ga Oktoba, 2025, jami’an tsaro sun samu sahihan bayanai cewa wanda ake zargin ya dawo cikin garin Makurdi domin kaddamar da wani sabon hari. 

Sai jami’an ‘yan sanda suka bi sahonsa, inda aka yi musayar wuta tsakaninsa da jami’an tsaro.

A lokacin arangamar, Saater Aii ya samu raunuka na harbin bindiga, kuma aka garzaya da shi asibitin koyarwa na Jami’ar jihar Benue, Benue State University Teaching Hospital, inda daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

Jami’an tsaro sun kwace bindiga kirar AK-47, bindigar gida (locally made gun), harsasai 7.62mm masu rai, da SIM cards guda bakwai daga hannunsa.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar ta bukaci jama’a da su guji aikata laifuka tare da taimaka wa jami’an tsaro da bayanai masu amfani domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin jihar.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments